Bayan kama ni da kwarto, mijina yana ta gwangwaje ni da kyautuka, Matar aure

Publish date: 2024-09-20

- Mijina ya fara yi min kyautuka na musamman bayan ya kama ni dare-dare a gado da kwarto, cewar wata mata aure

- Har alkawarin tafiya da ita kasar ketare yayi don su sha shagalin kirsimeti tare, bayan ya umarci kwartonta da ya tafi

- Yanzu haka ta shiga zullumin kada bayan sun tafi ya dauki wani mummunan mataki a kanta, shine take neman shawara

Wani mutum dan South Africa ya kwantar da hankalinsa bayan ya kama matarsa da kwarto a gadonsu na sunnah, ya kuma zage wurin bata kyaututtuka na ban mamaki.

Matar ta wallafa a kafar sada zumunta tana bukatar jama'a su bata shawara a kan rudanin da ta shiga, jaridar The Nation ta wallafa.

Ta ce mijinta ya kama ta dare-dare a kan gado tare da kwarto suna lalata, maimakon yayi mata kaca-kaca, sai ya fara yi mata salo iri-iri na soyayya, kuma ya umarci kwartonta ya sanya sutturarsa ya wuce abinsa.

A cewarta, ta yi zaton mijinta zai dauki tsauraran matakai a kanta, amma sai ya nuna mata cewa ba komai bane, hasali ma, ya koma bata kyautuka na musamman.

KU KARANTA: Fada a kan budurwa: An kashe mutum 1, jama'a masu yawa sun jigata

A cewar matar, mijinta ya tsiri yi mata kyautuka iri-iri tun bayan ya kama ta da kwarton, sai dai hakan ya saka ta a zullumi.

Ta bayyana yadda ta shiga tsananin tashin hankali bayan mijinta ya fara shirye-shiryen tafiya tare da ita kasashen ketare kafin lokacin bikin kirsimeti, sai dai, cike take da tsoro don kada ya dauki wani mummunan mataki a kanta idan sun tafi.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka manoma 7, sun sace mutum 30 a Katsina

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Olusegun ya bayyana irin bakar wahalar da ya fuskanta a soyayya lokacin yana daukar albashin N20,000.

Saurayin ya wallafa labarin abinda ya faru tsakanin shi da budurwarsa a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

A cewarsa, sun dan fita yawon shakatawa da shi da budurwarsa, ya siya wa kansa ruwa, ita kuma budurwar ta bukaci abincin N4500.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9knFvcG9lYq%2BixcCnZKSZnZZ6r7WMnZhmo6eWv7W7jKago6Gelnq6rc2aZK2ZXZzEorrGsJijnV2jtm6wwGaispmlqcKsrYymmK2ZomKutr7EZ5%2BtpZw%3D